in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun "hanyar siliki" ya cimma nasarar kulla kwangilar farko
2015-04-22 10:56:22 cri

Bayan da bankin zuba jari na Asiya AIIB ya tabbatar da kasashe mambobinsa na rukunin farko a kwanakin baya, asusun "hanyar siliki" da kasar Sin ta warewa dalar Amurka biliyan 40, ta kafa ya cimma nasarar kulla kwangilar farko.

A Litinin din farkon wannan mako ne asusun na "hanyar siliki", da kamfanin Sanxia, da kwamitin kula da harkokin kamfanonin samar da wutar lantarki, da samar da kayayyakin more rayuwa masu zaman kansu na kasar Pakistan, sun kulla yarjejeniyar "gudanar da aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa cikin hadin gwiwa".

Wannan dai shi ne aikin farko da asusun ya zuba jari cikinsa a kasashen waje, wanda ya shaida cewa, asusun ya samu ci gaba a fannin zuba jari. An ba da labarin cewa, za a fara gina tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa daga karshen wannan shekara, aikin da za a kammala nan da shekarar 2020, wanda wa'adinsa zai kai shekaru 30, kafin daga bisani a mika shi zuwa gwamnatin kasar Pakistan.

Mai ba da taimako ga shugaban hukumar hada-hadar kudi ta kwalejin kimiyya na al'ummar kasar Sin Yang Tao, ya ce asusun "hanyar siliki" ya zuba jari ga aikin gina tashar wutar lantarki a Pakistan, a matsayin sabuwar hanyar da aka kirkiro ta samar da kayayyakin more rayuwa tsakanin kasashen duniya. Ta wannan hanya kuma ake sa ran karin hukumomin hada-hadar kudi za su shiga cikin wannan aiki, domin inganta karin ayyukan kasuwanci masu kawo riba. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China