in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin ziri daya da hanya daya ba abu ne da kowace kasa za ta iya yin amfani da shi domin cimma burin siyasa
2015-05-22 10:08:55 cri

Jakadan kasar Sin dake kasar Birtaniya Liu Xiaoming ya furta a jiya Alhamis cewa, wasu kasashen da suka ci gaba ba sa yi wa kasar Sin adalci, inda suke nuna cewa, kasar Sin ta bullo da shirin ziri daya da hanya daya ne da nufin raya siyasa a kasashen dake makwabtaka da ita. Amma a hakika, shirin ba wata manufa ba ce da za ta amfani da ita, illa gudummawa ce da kasar Sin ta gabatar wa duniya.

Mr. Liu ya ce, shirin bai shafi tsaron kasa da matakan soja da kuma sauran batutuwan da ake nuna bambancin ra'ayi a kai ba, a hakika, shiri ne da ya kunshi ayyukan hadin gwiwar tattalin arziki da musayar al'adu. Ban da haka kuma, shirin ya sa kasashen da abin ya shafa su kara musayar ra'ayi da hadin kai, shi ya sa, ko shakka babu zai ba da kwarin gwiwa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, tare da kiyaye zaman lafiya.

Kazalika, Mr. Liu ya ce, akwai wasu da ke bayyana cewa, kasar Sin tana fatan sake kafa tsarin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa da habaka karfinta a duniya ta hanyar amfani da wannan shiri. Amma a zahiri, shirin ba zai mamaye tsoffin tsare-tsaren hadin gwiwa a yankin ba, sai dai ma ya sa kaimi ga kasashen dake kan hanyar siliki da su yi amfani da kwarewarsu domin kara kawo moriyar juna.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China