Benin za ta kara karfin samar da wutar lantarki zuwa megawattheure (MWH) 352 nan da karshen shekarar 2018
Gwamnatin kasar Benin ta dauki niyyar kara karfin kasa na samar da wutar lantarki zuwa megawattheure (MWH) 352 nan da karshen shekarar 2018, domin warware baki daya karancin wutar lantarki da kuma kawo karshen katsewar wutar lantarki da ake fuskatanta a kai a kai, in ji wata sanarwar gwamnatin kasar a ranar Asabar a birnin Cotonou. A cewar wannan majiya, domin warware matsalar wutar lantarki da daukewar wuta da ake fama da ita baki daya, gwamnatin Benin ta bullo da wani babban shiri na kawar da daukewar wuta nan da karshen shekarar 2016 kana kuma na samun wadatar wutar lantarki nan da shekaru biyu masu zuwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku