Benin: Sabon shugaban kasa yayi alkawarin girma kundin kasa da yaki da ta'addanci
Patrice Talon, wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Benin na ranar 20 ga watan Maris da ya gabata tare da kashi 65.37 cikin 100 na kuri'un da ya samu, an rantsar da shi a matsayin shugaban Benin a ranar Laraba a Porto-Novo, hedkwatar siyasar kasar Benin, ya shelanta niyyar ta girmama kundin tsarin mulkin ranar 11 ga watan Disamban shekarar 1990, na tsawon wa'adin mulkinsa na shekaru biyar daga shekarar 2016 zuwa 2021, tare da kuma bayyana niyyarsa gaban mambobin kotun kolin kasar na cika alkawuran ayyukan kasa da aka mika masa, tare da natsewa kan moriyar kasa da girmama 'yancin dan adam, da maida dukkan karfinsa ga nema da bunkasa alheri, zaman lafiya da hadin kan kasa. Haka kuma yayi alkawarin kare 'yancin fadin kasar Benin a wannan wa'adinsa na mulki da natsewa wajen kai kasar bisa tudun mun tsira da bautawa jama'a yadda ya kamata. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku