Kwamitin zabe na kasar Benin mai zaman kansa ya sanar a jiya Litinin 21 ga wata cewa, dan takara Patrice Talon ya ci zaben shugaban kasar.
Shugaban kwamitin zaben ya bayyana cewa, bisa sakamakon kidayar kuri'un da aka kada, Patrice Talon ya samu kuri'u miliyan 2 da dubu 10 a yayin jefa kuri'u na zagaye na biyu, wadanda suka dauki kashi 65.39 cikin dari na jimillar kuri'un da aka jefa, sannan abokin hamayyar shi kuma firaministan kasar Lionel Zinsou ya samu kuri'un da suka dauki kashi 34.61 cikin dari.
Lionel Zinsou ya tabbatar da cin tura a zaben, kuma ya taya wa Patrice Talon murnar cin zaben.(Lami)