An kulla yarjejeniyar hadin gwiwar ne a ranar Lahadi, inda shugaban jami'ar ta MKU, farfesa Simon Gicharu, da dokta Fengchi Luan, jami'i mai kula da aikin horar da dalibai na kasa da kasa a Jami'ar Fasahar Sarrafa Albarkatun Mai ta kasar Sin suka sanya hannu kan yarjejeniya a madadin bangarorin 2, a birnin Nairobi.
Bisa wanna yarjejeniyar, jami'o'in 2 za su fara musayar dalibai, tare da gudanar da ayyukan nazari kan kimiyya da fasaha cikin hadin gwiwa.
A cewar farfesa Simon Gicharu, yarjejeniyar za ta samar da makoma mai kyau ga dalibai da malamai na jami'ar ta MKU, ganin yadda kasar Kenya gami da sauran kasashen Afirka suke da dimbin albarkatun kasa, amma karancin kwararru a fannin sarrafa su ke haifar da koma baya wajen cin gajiyar albarkatun.
Jami'ar Fasahar Sarrafa Albarkatun Mai ta kasar Sin ita ce jami'a mafi shahara a fannin tarin kwararru a bangaren nazarin fasahohin sarrafa danyen mai, an kuma kafa ta tun cikin shekarar 1953. (Bello Wang)