Kenya za ta ci gaba da gina katangar a kan iyakarta da Somaliya
Kenya ta tabbatar a ranar Lahadi da sake ci gaba da aikin gina katangar tsaro a tsawon kan iyakarta da kasar Somaliya domin dakatar da kutse daga wata kasa zuwa wata kasa na mayakan kungiyar ta'addancin kasar Somaliya ta Al-Shabaab. Ministan cikin gidan Kenya, Joseph Nkaissery ya tabbatar da cewa aikin gina katangar tsaro mai tsawon kilomita 700 a kan iyaka tsakanin Kenya da Somaliya ta Mandera a arewacin Kenya dake Kiunga, a bangaren gasbashin kasar, zai taimaka wajen hana mayakan Al-Shabaab kutsawa cikin kasar tun daga Somaliya, da kuma hana mutanen da ba a bukata dake shiga kasar ta bayan fage. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku