Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai, babban sakatare a ofishin ma'aikatar man fetur da makamashi Charles Keter, ya ce kamfanin hakar mai na Tullow ne ya gano danyen man, yayin da yake aiki a sashen Cheptuket . Sai dai ya ce sai a nan gaba ne za a tantance ko yawan man zai kai a rika hako shi domin sayarwa.
Tuni dai kamfanin na Tullow ya gano wata mahakar man dake Lokichar, wadda za ta iya samar da danyen mai da ya kai kusan ganga miliyan 600, ita ma dai a yankin na arewacin Kenya
A wani ci gaban kuma, Mr. Keter ya ce yana da kwarin gwiwa game da cimma nasarar aikin shimfida bututun mai, wanda zai hada kasashen Kenya da Uganda, yana mai cewa Kenya ta tanaji tallafi na musamman ga Uganda, ciki hadda saukaka wa kasar haraji, kasa da abun da ya dace Kenya ta caza wajen tura man Uganda zuwa teku.