Kenya za ta kona wadannan hauran giwa, na fiye da ton 120, a yayin wani bikin da zai gudana a ranakun 29 zuwa 30 ga watan Afrilu, domin nuna niyyarta na "babu sassauci ga masu farauta ba bisa doka ba da kuma fataucin hauran giwa"
Ministar muhalli, madam Judy Wakhungu, ta bayyana a ranar Laraba cewa "karuwar adadin kananan giwaye" a cikin kebabbun gandun daji, wata alama ce ta samun cigaba.
Farautar giwaye ba bisa doka ba ta ragu da 184 a shekarar 2012 zuwa 96 a shekarar 2015, a cewar jami'in.
Ma'aikatun kare albarkatun gandun daji na kasar kenya (KWS) sun bunkasa wani shirin kula da kiyaye bisa tsawon shekaru 10 domin kare giwayen kasar, in ji madam Wakhungu.
A cewar jami'ar, giwayen Afrika na fuskantar barazanar da ta hada da farauta ba bisa doka ba, rikicin kabilu, raguwar filayen gandun daji, da kuma karuwar al'umma a wasu yankuna. Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta zai halarci bikin lalata hauran giwar, in ji madam Wakhungu. (Maman Ada)
Kenya za ta lalata hauran giwa fiye da ton 120 a karshen watan Afrilu
Kasar Kenya ta bayyana samun cigaba wajen yaki da masu farautar namun daji ba bisa doka ba, a yayin da take shirin shirya lalata hauran giwa masu tarin yawa a karshen wannan wata.