Yayin da ya gana da shugaba Kenyatta, mista Zhang Dejiang ya ce, kasar Sin da kasashen Afrika abokan hulda ne. A karkashin sabon yanayin da ake ciki, inganta zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da karfafa hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu na da muhimmanci sosai. A yayin taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika da aka yi a birnin Johannesburg, shugabannin Sin da Afrika sun tsara alkiblar raya hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin biyu. Kenya muhimmiyar abokiyar kasar Sin ce, kasashen biyu suna girmama juna da amincewa juna, kuma ana samun hadin gwiwa mai gamsarwa daga dukkan fannoni, abun da ya kafa misali game da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Tare da fatan bangarorin biyu za su yi amfani da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin, don yin amfani da fiffikonsu, da bunkasa sana'o'in kasashen biyu da inganta hadin gwiwa a fannonin jiragen kasa, tashoshin teku da ma sauran muhimman ababen more rayuwa, da raya masana'antu da kafa yankin raya tattalin arziki na musamman, don yalwata dangantakar abokantaka daga duk fannoni tsakanin kasar Sin da kasar Kenya.
A nasa bangare shugaba Kenyatta ya ce, kasar Kenya tana kaunar dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ta dora muhimmanci sosai game da hakikanin hadin gwiwa da kasar Sin, tana fatan koyon fasahohin ci gaba da Sin ta samu. Shugaban Xi ya gabatar da shirin hadin gwiwa a fannoni 10, abun da ya dace da manyan tsare-tsaren raya kasar Kenya. Kasar Kenya tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin, da ci gaba da gudanar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli, kuma yana fatan hukumomin tsara dokoki na kasashen biyu za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin mulki da mu'amala a tsakanin jam'iyyun kasashen biyu.
A yayin shawarwarinsa da shugaban majalisar dokokin kasar Kenya Justin Muturi da shugaban majalisar dattijai Ekwee Ethuro, Zhang Dejiang ya ce, inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsara dokokin kasashen biyu, abu ne da zai ba da tabbaci ga raya dangantakar kasashen biyu, yana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da kafa amincewar juna a fannin siyasa da kara mu'amala don daga matsayin hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)