Kakakin hukumar yankin Middle Shebelle, mista Da'ud Haji Iro, ya bayyana cewa dakarun hadin gwiwa sun karbi ikon yankunan Runir-Dieu, Nur-Dugle, Ad-Adeyles dake yankin Moyen-Shebelle, bayan samame kan mayakan Al-Shabaab a safiyar ranar Abasar.
Dakarun SCN da AMISOM sun gudanar cikin hadin gwiwa wani samame kan kungiyar ta'addancin dake wannan yankin, kuma dukkan yankunan da aka karba daga hannun mayakan Al-Shabaab suna cikin kwanciyar hankali yanzu, in ji mista Iro.
An samu tirjiya daga wannan kungiya a yayin samamen, amma ba a samu asarar rayuka ba. Dakarun hadin gwiwa za su kwato bada jimawa ba sauran yankin daga hannun mayakan Al-Shabaab, in ji jami'in.
AMISOM ta fara jibge sojojinta a kasar Somaliya a shekarar 2007, dake kunshe da sojojin Kenya, Habasha, Uganda da Burundi. Tare da taimakonta, rundunar sojojin Somaliya sun samu nasara sosai kan Al-Shabaab da ta mamaye babban yankin tsakiyar Somaliya da na arewaci. (Maman Ada)