in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bukaci a inganta yunkurin shimfida zaman lafiya a Somaliya
2016-04-20 11:36:10 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya fada a jiya Talata cewa, kasar Somaliya na ci gaba da fuskantar mummunan hali ta fannin tsaro da jin kai, ya kamata kasashe daban daban su ci gaba da inganta aikin shimfida zaman lafiya a kasar Somaliya.

Mr. Wu ya bayyana a gun wani taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a wannan rana game da batun Somaliya, inda ya ce za a yi babban zabe a kasar Somaliya a wannan shekara, hakan ya sa aikin shimfida zaman lafiya a kasar ya shiga wani muhimmin yanayi. Gwamnatin Somaliya a nata bangaren tana kokarin samun sulhu a tsakanin sassa daban daban na zaman al'umma da yaki da ta'addanci, da kuma inganta kafa tsarin tarayya domin tabbatar da burin kasa na shekarar 2016. A sa'i daya kuma, kasar na ci gaba da fama da rashin tsaro da jin kai, shi ya sa cimma burin tabbatar da zaman lafiya a kasar yake da wuya sosai.

Ya kara da cewa, kasar Sin da kasashen Afrika suna da moriya iri daya. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afrika ciki har da Somaliya wajen tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa Sin da kasashen Afrika, za ta taimakawa kasashen Afrika wajen kyautata zaman rayuwar jama'a da kara karfinsu na samun bunkasuwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China