A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis da yamma, mambobin kwamitin tsaro sun jaddada yin allawadai da hare hare da kuma shigar da yara kanana da kungiyar ta'addanci ta Al-Chabaab take yi tare da kuma jinjinawa tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake kasar Somliya (AMISOM) da rundunar sojojin kasar Somaliya game da kokarin rage barazanar da kungiyar ta Al-Chabaab.
Haka kuma mambobin kwamitin sun jaddada muhimmancin ci gaba da ayyukan kai samame na AMISOM da rundunar sojojin Somaliya kan mayakan Al-Chabab, bisa tsarin hada kai yadda ya kamata da kuma mutunta 'yancin jin kai na kasa da kasa da kare fararen hula. (Maman Ada)