Mr. Francisco wanda ke tsokaci gaban taron masu ruwa da tsaki a birnin Mogadishu, ya ce ya zama wajibi a dauki karin matakan kariya ga matasan Somaliya, ta yadda ba za su fada tarkon wanke kwakwale da Al-Shabaab ke danawa ba, matakin da a cewar sa na da matukar muhimmanci wajen yaki da tada kayar baya a yankin baki daya.
Ya kuma kara da cewa tawagar AMISOM dake aikin wanzar da zaman lafiya tare da sauran masu tallafa mata, za su ci gaba da karfafa ayyukan su na wanzar da doka da Oda a kasar. Ya ce yana da kyakkyawan fatan cimma nasarar yakin da ake yi da kungiyar Al-Shabaab, musamman idan har al'ummar kasar suka ci gaba da marawa matakan da ake dauka baya yadda ya kamata.
Mr. Francisco ya kara da cewa, yayin da ake daukar matakan bunkasa ilimi, da samar da matsugunni, da abinci ga matasa domin kare su daga shiga kungiyar ta Al-Shabaab, ya zama wajibi kuma a rubanya kokari wajen yaki da fatara, da rashin ayyukan yi, da maida wasu sassa saniyar ware, matsalolin da kwararru ke alakantawa da musabbabin shigar wasu daga matasan cikin wannan kungiya mai matukar hadari.
Daga nan sai ya jaddada aniyar tawagar AMISOM ta ci gaba da yaki da 'yan ta'adda a Somaliya, duk kuwa da tarin kalubale da aikin ke fuskanta. A daya bangaren kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su kara yawan taimakon da suke baiwa wannan muhimmin aiki.(Saminu Alhassan)