AMISOM ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa rundunonin hadin gwiwa sun karbe ikon birnin bayan wani babban samaman da suka kai kan mayakan kungiyar Al-Chabab.
Dakarun hadin gwiwa sun yi bata kashi da mayakan a Moqokori da Mahaas a yankin Hiiraan, in wannan sanarwa. Mazauna wurin da suka bar birnin domin zama a wuraren dake kewaye sun fara komawa muhallinsu sannu a hankali a Adan Yabaal.
A cewar sanarwar, mazauna wurin sun fuskanci karancin kayayyaki, musammun ma ruwan sha, ganin cewa mayakan Al-Chabab sun lalata yankunan da al'umma suke zama da lalata gine gine, da kona kayayyakin abinci da lalata janareta da ake amfani da shi domin janyo ruwa daga cikin rijiyoyi dake aiki kafin su janye daga birnin.
AMISOM da rundunar Somaliya suna aiki tare da gwamnatin Somaliya domin mai do da tsarin samar da ruwan sha da sauran muhimman ayyuka a Adan Yabaal. (Maman Ada)