Jakadan kasar Sin a Kenya Liu Xianfa, da babban jami'in kasar Kenya na daga cikin mahalarta taron wanda fitattun makadan kasar Sin suka nishadantar da masu kallo da wakoki nau'i dabam dabam a lokacin taron.
A jawabinsa na bude taro Liu, ya fada cewar, nuna bajinta a fannin wake wake na daga cikin jerin fannoni dake kara karfafa dangantakar al'adu tsakanin kasashen Sin da Kenya.
Ofishin jakadancin kasar Sin da hadin gwiwar kwararun 'yan kasuwar Sin mazauna kasar Kenya ne suka kaddamar da shirin, a matsayin wani bangare na karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A cewar mista Liu, kasar Sin tana hadin gwiwa da Kenya a muhimman fannoni da suka hada da ilmi da al'adu da cinikayya da samar da muhimman ababan more rayuwa da kuma fannin kiyaye muhalli.
Charles Sunkuli, babban sakatare a ma'aikatar muhalli da albarkatun kasa na kasar Kenya ya bayyana cewar, bikin nuna wakokin na birnin Nairobi, alama ce dake nuna irin karfin alakar dangantakar kasar Sin da Kenya a fannin diplomasiyya da raya al'adu, kuma gwamnati Kenya za ta ci gaba da hada gwiwa da kasar Sin, don bunkasa ci gaban fannonin ilmi da al'adu da kare muhalli. (Ahmad Fagam)