in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Benin na shirin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa
2016-03-15 19:41:02 cri

A ranar Lahadi mai zuwa ne firaministan kasar Benin Lionel Zinson zai fafata da hamshakin dan kasuwan kasar Patrice Talon a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da zai gudana a ranar 20 ga watan Maris.

Shi dai Zinson wanda ke samun goyon bayan shugaban kasar mai ci, ya kasance a kan gaba tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar 32, inda ya samu kashi 28.4 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben, yayin da mutumin da yake kalubalantarsa a zaben Talon ya samu kashi 24.8 cikin 100.

Har zuwa jiya Litinin 'yan takara 24 da suka sha kaye a zagayen farko na zaben ne ke goyon bayan Talon, wadanda suka hada da Sebastien Ajayon, wanda ya samu kimanin kashi 23 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Sama da masu kada kuri'a miliyan 3 da aka yi wa rijista ne suka kada kuru'unsu a zagayen farko na zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar 6 ga watan Maris.

Duk wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben tsakanin 'yan takarar biyu, shi ne zai maye gurbin shugaba kasar mai ci Yayi Boni, wanda wa'adin mulkinsa zai kare a karshen watan Afrilun wannan shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China