A cewar darektan gudanarwa na ma'aikatar kudi da tattalin arziki, mista Servais Adjovi, cibiyar za ta taimakawa wajen kafa tsarin kasa na kula da bayanan filaye mai kyau, har ma da bada ra'ayi game da sayar da filaye a karkara.
Muhimman kalubalolin dake jiran wannan cibiyar kasa su ne wadanda suka shafi kula da filaye ta fuskar tsaro da kuma bada kulawa ga 'yancin zaman jama'a a dukkan fadin kasar Benin tare da neman amincewar al'ummomi, in ji mista Servais Adjovi. (Maman Ada)