Bisa kwarya-kwaryar sakamakon da wata hukumar binciken ra'ayoyin jama'a ta samar kan zagaye na biyu na babban zaben kasar Benin, wanda aka gudanar a ranar 20 ga wata, ya yiwu dan takara mai zaman kan sa Patrice Talon ya shige gaba da kaso sama da 60 bisa 100 na kuri'un da aka kada, don haka mai yiwuwa ne ya lashe zaben.
Dan takarar dake fafatawa da Mr. Talon a zagayen na biyu, kuma firaministan kasar Lionel Zinsou, ya amince da shan kaye a shafinsa na Facebook, kuma tuni ya taya Talon murna.
Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar dai ba ta kai ga fidda cikakken sakamakon zaben zagaye na biyu a hukunce ba.(Bako)