Majo Janar Francis Okello, shi ne ya jagoranci tawagar jami'an na AU, ya bayyana cewar tawagar tana gudanar da aikin bibiyar jami'an nata ne domin tantance yankunan da suka fi bukatar a kara yawan jami'an masu aikin wanzar da zaman lafiyar.
A wata sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi a Mogadishu Okello, ya bayyana cewar sun ziyarci kasar ne domin duba yanayin tanadin da jami'an nasu suka yi domin maido da zaman lafiya a kasar.
Ya kara da cewar a watan Augustan shekarar data gabata, tawagar ta AMISOM da helkwatar kungiyar ta AU, sun gabatar da jadawalin yadda zasu gudanar da ayyukan su wato CONOPS, don haka ne tawagar ta ziyarce su domin duba irin matakin da suka kai game da aikin warware rikicin siyasar kasar.
A cewar Okello, tawagar tana nazari game da yadda za'a kara taimakawa AMISOM da sauran hukumomin tsaro a kasar ta Somali a yakin da suke yi da mayakan na Al-Shabaab.
Bugu da kari, daga cikin dalilan ziyarar jami'an, har da batun shirin tunkarar zabukan shugaban kasa dana majalisar dokokin kasar da ake sa ran gudunarwa a cikin wannan shekara. (Ahmad Fagam)