in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron Somaliya ta sake karbe ikon yankunan da Al-Shabaab ta mamaye
2016-02-14 10:52:55 cri
Rahotanni daga kafafen yada labaran Somaliya na cewa, rundunar tsaron kasar ta sake kwace wasu garurruwa da kauyuka dake tsakiyar kudancin kasar da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab ta kwace.

Wani jami'in jihar Gobolkashabeellahadhexe dake yankunan kudu maso gabashin kasar ya fada wa wakilinmu cewa, a cikin 'yan kwanakin nan, rundunar tsaron kasar da sojojin kungiyar AU sun dauki matakan aikin soji na hadin gwiwa, inda suka sake mamaye wani gari da wasu kauyuka da ke da nisan kilomita 40 da Jowhar wato cibiyar jihar.

A wata sanarwar kuma, wasu jami'an kananan hukumomin kasar sun bayyana cewa, a sa'i daya kuma an maido da wasu yankunan da ke jihar Gobolkahiran.

Jami'ai 'yan sanda sun bayyana cewa, rundunar tsaro da sojojin kungiyar AU tana farfado da tsaro a wuraren, ya zuwa yanzu, an damke mutane 2 da ake zargi da hannu cikin harin ta'addanci wadanda ke da alaka da Al-shabaab.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China