AU ta nuna yabo kan ci gaban kokarin zaman lafiya a Somaliya
Kungiyar tarayyar Afrika ta nuna yabo a ranar Litinin game da ci gaban da aka samu domin kawo zaman lafiya a kasar Somaliya duk karuwar hare haren ta'addanci na kungiyar mayakan kishin islama na Al-Shabab. Manzon musammun na kungiyar AU a Somaliya kana kuma darektan tawagar kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM), mista Francisco Madeira, ya nuna gamsuwarsa game da ci gaban da aka cimma a Somaliya tun zuwan dakarun farko na AU a birnin Mogadiscio na kasar Somaliya din a shekarar 2007."AMISOM, tare taimakon ayyukan soja na hadin gwiwa, ta kafa wani yanayin da aka samar da wani shirin siyasa, musamman sasanta 'yan kasa da kuma kafuwar wata kasa dake cigaba da kasancewa gaskiya sannu a hankali da dorewa", in ji jami'in a yayin wani zaman taro na kwamitin daidaita ayyukan soja (COMM) na AMISON a birnin Nairobi na kasar Kenya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku