Somaliya ta kaddamar da wani sabon shiri na siyasar ketare bayan shekaru 20 na yakin basasa
Kasar Somaliya ta kaddamar a ranar Lahadi da wani sabon shiri na siyasar waje na baki daya domin jagorantar huldarta tare da kasashen duniya, kan muhimman batutuwa kamar kasuwanci da kuma yaki da ta'addanci. A cewar wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin wajen Somaliya, kaddamar da sabon shiri na siyasar waje na daya daga cikin wani muradi mafi girma domin tabbatar da cewa kasar ta kasance wata mai taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasa da kasa.
Siyasar waje ta kasar Somaliya an gina ta bisa muhimman ginshikai na bunkasa dorewar zaman lafiya da tsaro a cikin kasa, shiyya da kuma kasa da kasa tare da taimakon halartar gaba daya a cikin diplomasiyyar huldar dangantaka, a cewar wannan sanarwa ta ma'aikatar harkokin wajen Somaliya. (Maman Ada)