Mataimakin faraministan ya bayyana cewa, sabuwar rundunar sojojin ruwan za ta taka rawa kan muhimman ayyukan kare albarkatun ruwan kasar, da aka lalata tun shekaru da dama da suka gabata, dalilin rashin wata tsayayyar rundunar ruwa a kasar Somaliya.
"Wannan ya kasance wani nauyi na rundunar sojojin ruwanmu na tabbatar da kare fadin ruwa da albarkatun ruwan kasar daga duk wani aikin kamun kifin da ba bisa doka ba. Za mu himmatnuwa kai da kafa wajen sake gina rundunonin ruwa ta yadda za su cika aikinsu yadda ya kamata," in ji mista Arte a birnin Mogadiscio a yayin bikin cikon shekaru 51 na rundunar ruwan Somaliya.
Jami'in Somaliyan ya yi wadannan kalamai bisa ga damuwar da hukumomin kasar suke nunawa game da dawowar ayyukan fashin teku a cikin ruwan Somaliya, dalilin karuwar kamun kifi ba bisa doka ba daga wasu jiragen ruwa na waje. (Maman Ada)