Babban bankin na Afrika ta Kudu ya fada cewar ana saran tattalin arziki kasar zai karu ne bisa hasashen samun bunkasuwa a kayayyakin da ake samarwa na cikin gida, inda akayi hasashen karuwar sa zuwa kashi 1 da digo 6 a shekarar 2017, kasa da yadda akayi hasashe da farko na samun karuwar kashi 2 da digo 1 cikin 100.
Babban bankin kasar ya fada bayan kammala zaman kwamitin al'amurran kudin kasar MPC cewar, bisa hasashen da aka yi, karuwar tattalin arzikin kasar a shekarar 2015 ta kai kashi 1 da digo 3 cikin 100.
Yanzu dai hasashen da bankin yayi ya gamu da nakasu, na samun karuwar kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje da kashi 1.9 ya koma kashi 1.5 a 2016, sannan daga yiwuwar karuwar kashi 2.1 ya koma kashi 1.6 a 2017. (Ahmad Fagam)