Bayan share fage na tsawon kwanaki fiye da dari 8, a yau Jumma'a 25 ga wata, a hukumance aka kafa bankin zuba jari kan ayyukan more rayuwar jama'a na Asiya wato AIIB, wanda kasar Sin ta yi kirar kafa ta kuma kasashe 57 suka kafa cikin hadin gwiwa. Wannan shi ne hukumar kudi ta farko a duniya, wadda kasar Sin ta yi kira a kafa ta a tsakanin kasa da kasa.
Ya zuwa ranar Jumma'an nan 25 ga wata, kasashen Sin, Singapore da sauran kasashe 15 sun amince da yarjejeniyar bankin AIIB, tare da gabatar da takardar amincewa, yawan jarin da suke mallaka ya wuce rabin jimillar jarin bankin.
Bisa shirin kafa bankin, za a gudanar da bikin kaddamar da bankin daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Janairu mai kamawa a nan Beijing, inda za a zabi shugaban bankin, da darektocin yankuna a yayin babban taron kafuwar majalisar zartaswa da taron manyan darektocin zartarwa, tare da dudduba da zartas da wasu muhimman takardun da ke shafar ayyukan bankin, harkokin kudi da dai sauransu, a kokarin share fagen kaddamar da ayyukan bankin a hukumance. (Tasallah Yuan)