in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron G20 zai sa kaimi ga kawar da ta'addanci, in ji mataimakin ministan kudi na Sin
2015-11-15 14:05:47 cri
Jiya Asabar 14 ga wata, mataimakin ministan kudi na Sin, Zhu Guangyao ya jaddada a birnin Antalya na Turkiya cewa, taron shugabannin kungiyar G20 a karo na 10 zai yi kokarin sa kaimi ga raya tattalin arzikin kasashen duniya, da cimma burin neman samun bunkasuwa da kawar da talauci, hakan kuma zai sa kaimi ga kawar da ta'addanci a duniya baki daya.

A taron manema labaru da aka shirya, mista Zhu ya bayyana cewa, harin ta'addancin da aka kai a birnin Paris na Faransa a daren Jumma'a 13 ga wata ya sake bayyana cewa, ta'addanci zai kasance abokin gaba na bil'adam baki daya. A yayin da ake fuskantar barazanar, tabbatar da cimma nasarar taron koli na G20 a birnin Antalya zai yi ma'ana sosai ga mambobin kungiyar G20.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China