in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Antalya domin halartar taron G20 karo na 10
2015-11-15 12:15:22 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa jiya Asabar a birnin Antalya na kasar Turkiya, domin halartar taron G20 karo na 10, da aka tsaida shirya daga 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Shugaban Sin zai sanar da shugabannin duniya kan kokarin da kasarsa ta bayar wajen zurfafa gyare gyare da kuma gina wani tattalin arziki na bude kofa, haka kuma da hangen gwamnatin kasar Sin game da shirya taron G20 na shekara mai zuwa.

Haha kuma zai yi amfani da wannan dama ta ziyararsa a Antalya domin tattaunawa tare da shugabannin sauran kasashe, musammun na sauran mambobin kungiyar BRICS.

Bayan taron na G20, shugaba Xi Jinping zai wuce Manila domin halartar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 23, da za'a bude daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Nuwamba.

Bisa taken "Yunkuri guda domin wani tattalin arziki mai dorewa da karfi", taron na Antalya nada manufar tallafawa wata amincewar duniya da tabbatar da wata bunkasuwa mai karfi da dorewa da daidaituwar tattalin arzikin duniya.

Haka zalika, shugabannin zasu yi nazari kan gyare gyaren tsarin harkokin kudi na duniya, da kasuwanci, makamashi, yaki da cin hanci, matsalar 'yan gudun hijira da ta'addanci.

G20 ya kasance wani dandali kan dangantakar tattalin arziki da kudi ta duniya dake tattara manyan kasashe mafi karfin tattalin arziki da masu tasowa, wanda kuma yake wakiltar kimanin kashi 85 cikin 100 na GDP na duniya, da kashi 80 cikin 100 na kasuwancin duniya da kuma kwashe kashi 2 cikin 3 na al'ummar duniya.

Kasar Sin zata karbi shugabancin G20 na shekarar 2016. Kuma, shugaba Xi Jinping zai sanar a Antalya, da birnin kasar Sin da zai karbi taron G20 karo na 11 da kuma ranar da zai iya taron. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China