in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayani kan halartar shugaban kasar Sin taron G20 da na APEC
2015-11-11 10:11:04 cri
A jiya Talata ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru, inda mataimakin minista Li Baodong ya yi bayani, game da batutuwan da suka shafi taron shugabanni karo na 10 na kungiyar G20, da kwarya-kwaryar taron koli karo na 23 na kungiyar APEC wadanda shugaba Xi Jinping na kasar zai halarta.

Li ya bayyana cewa, za a gudanar da taron G20 karo na 10 ne tsakanin ranekun 15 zuwa 16 ga watan nan a birnin Antalya na kasar Turkiya. A lokacin, shugaba Xi zai halarci dukkan ayyukan taron na kolin, inda zai yi bayani sosai kan ra'ayinsa game da yanayin tattalin arziki da duniya ke ciki, kana zai yi kira ga bangarori daban daban, game da bukatar hada kai da nufin fuskantar kalubale tare, da kuma neman sabuwar hanyar samun bunkasuwar.

Game da taron koli na APEC kuwa, Li ya bayyana cewa taron karo na 23 zai gudana ne tsakanin ranekun 18 zuwa 19 ga wannan wata a birnin Manila na kasar Philippines. Ya ce a yayin taron, shugaba Xi zai halarci taron shugabannin fannin masana'antu da cinikayya. Zai kuma gabatar da jawabi, inda zai bayyana ra'ayin kasar Sin game da hadin kai a shiyyar Asiya da Pasific, da ci gaban da aka samu wajen aiwatar da ayyukan da aka tsara a yayin taron APEC na Beijing, kana zai bayyana matakan da Sin ta dauka wajen zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da inganta kyautata tsarin tattalin arziki da dai sauransu.(Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China