Wakiliyar musamman na babban sakataren MDD Karine Landgren da manyan jami'an tawagar musamman ta MDD dake kasar Liberia da hafsoshin tawagogin rundunonin kasa da kasa masu kiyaye zaman lafiya dake kasar Liberia da jami'an gwamnatin jihar Grand Gedeh fiye da 150 suka halarci bikin.
Madam Karine Landgren a jawabin ta wajen bikin ta yabawa sojojin Sin masu kiyaye zaman lafiya tana mai cewa, sojojin na kasar Sin sun yi kokarin gudanar da ayyuka ba tare da yin la'akari da kansu ba, sun bada gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da yaki da cutar Ebola a kasar Liberia, kuma su ne abin koyi ga dukkan sojojin kiyaye zaman lafiya. (Zainab)