in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda: Mutanen da suka tsira daga kisan kare dangi na adawa da wani hukuncin kotun Faransa
2015-10-08 10:50:28 cri
Mutanen da suka tsira daga kisan kare dangi na kasar Rwanda a shekarar 1994 sun bayyana rashin gamsuwarsu kan matakin wata kotun kasar Faransa na yin watsi da tuhume tuhume kan wani malamin cocin Rwanda da ake zargi da hannu cikin kisan kare dangin.

Kotun kasar Faransan ta yi watsi a ranar Talata da tuhume tuhume kan Wenceslas Munyeshyaka, wanda kotun kasar Rwanda ta tabbatar da laifin kan kisan kare dangi duk da cewa ba ya kasar. Daga bisani kotun kasa da kasa kan batun Rwanda dake da cibiya a kasar Tanzaniya ta mika takardun mista Munyeshyaka ne ga kotun kasar Faransa,inda mutumin yake zama yanzu.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China