Sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya jajantawa dangin wadanda suka rasu sakamakon tarzomar, kana ya lura da kokarin da shugaban kasar Afrika ta Kudu, da gwamnatinsa suka yi, domin kawo karshen tarzomar, da ma sanarwar da aka bayar game da batun.
Ban Ki-Moon ya yi maraba da kiraye-kirayen al'ummar Afrika ta Kudu na fatan rungumar zaman lafiya cikin jituwa tare da baki dake zaune a kasar. Kaza lika, ya bukaci a ci gaba da kokari wajen hana aukuwar hare-haren da aka kaiwa baki a nan gaba, gami da warware dukkanin matsaloli cikin lumana.
A karshen watan Maris ne dai tarzomar kyamar baki ta barke a birnin Durban dake Afrika ta Kudu, inda daga bisani kuma lamarin ya bazu zuwa sauran wurare. Wannan dai shi ne kyamar baki mafi muni da ya faru a Afrika ta Kudu tun daga shekarar 2008.
A ranar Talata ne dai ministar tsaron kasar Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta bayyana cewa, ta yanke shawarar tura sojoji zuwa wuraren da tarzomar ta auku, don gaggauta dakile ci gabanta. (Bako)