in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta yi allawadai da hare haren kyamar baki a Afrika ta Kudu
2015-04-18 15:59:14 cri
Gamayyar tattalin arzkin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi allawadai a ranar Jumma'a kan kisa, cin zarafi da kuma kyamar baki 'yan kasashen Afrika da ba su ji ba su gani ba a kasar Afrika ta Kudu.

A cikin wata sanarwar da aka sanya wa hannu a ranar Jumma'a, shugaban kungiyar ECOWAS, kuma shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bukaci gwamnatin Afrika ta Kudu da ta dauki matakan da suka wajaba domin kawo karshen hare haren kyamar baki dake ci gaba da karuwa a fadin kasar. Ya yi allawadai da cewa mutanen kasashe daban daban da suka sadaukar da rayukansu domin taimakawa 'yan kasar Afrika ta Kudu wajen yaki, kawar da kuma samun nasara kan wariyar launin fata, su ne a yanzu aka maida matsayin baki kuma ake ma kisan wulakanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China