Wasu 'yan bindiga da ake zaton mayakan Al-Shabaab ne sun halaka wani jami'in gwamnatin kasar Kenya a garin Wajir da ke kan iyaka a arewa maso gabashin kasar.
Jami'in 'yan sandan yankin Wajir Samuel Mukindia ya tabbatar da cewa, wasu 'yan bindiga sun harbe Mohamed Barre Abdullahi har lahira a kan hanyarsa ta dawowa gida daga masallaci. Kuma har yanzu ba a kai ga gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki da kuma manufarsu ba.
Kisan na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan da gwamnati ta dage dokar hana fita ta watanni biyu da aka sanya a shiyyar da ke iyaka da kasar Somaliya da yaki ya daidaita, a wani mataki na baiwa musulmi isasshen lokacin yin salar ashiyam da sauran Ibadu a watan Ramadan.
A baya ne dai gwamnati ta sanya dokar hana fita, sakamakon kashe wasu mutane 148 da mayakan Al-Shabaab suka yi ranar 2 ga watan Afrilu a jami'ar Garissa.(Ibrahim)