Kwamishinan yankin Alex Ole Nkonyo wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan sauran mutanen da ke da hannun a kashe-kashen da ya faru tsakanin al'ummomin Garre da Degodia da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 100.
Nkoyo ya ce, an kama jami'an yankunan Elmole, Hullow da Banisa da ke gundumar Banisa saboda gazawarsu ta shiga tsakanin a tashin hankalin da ya barke tsakanin kabilun biyu a makon da ya gabata inda har mutane 15 suka rasa rayukansu.
Garin Mandera dai ya sha fuskantar hare-hare daga mayakan Al-Shabaab da ke Somaliya da yaki ya tagayyara kana ta ke fama da fadan kabilanci tsakanin kabilun Degodia da Garre masu rinjaye da suka samu zaman lafiya a 'yan watannin da suka gabata.
Daga karshe kwamishinan ya bukaci kabilun da ke gaba da juna da su kai zuciya nesa, tare da hawa teburin sulhu a ko wane lokaci don warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu.(Ibrahim)