Rahoton ya yi nuni da cewa, ana bin cikakken tsarin dokoki wajen raya harkar yanar gizo a kasar Kenya, inda aka kayyade ka'idoji a fannonin ciniki da tabbatar da asalin masu sayen kayayyaki a kan internet. Ban da wannan kuma, gwmanatin kasar Kenya ta dora muhimmanci ga bunkasuwar fasahohin sadarwa, inda ta sanya wannan fanni a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da aka tsara don cimma burin shirin raya kasa na shekarar 2030. (Zainab)