An dai gabatar da wannan sanarwa ne yayin taron musamman na majalisar zartaswar kungiyar.
A watan Satumbar bara ne dai kungiyar WTO ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban a karo na farko, na yarjejeniyar birnin Bali, a taron ministocin kungiyar karo na tara, yarjejeniyar da ta tsara samar da saukin cinikayya wadda kuma ta ba da babbar gudummawa kan cinikayyar kasa da kasa.
Wannan yarjejeniya baya ga kasancewar ta hanyar kawo sauki ga cinikayya tsakanin kasa da kasa, a daya hannun kuma ta rage yawan kudaden da ake kashewa kan hakan. Da samar da karin guraben aikin yi, da kuma kara yawan kudin cinikayyar kasa da kasa.
Bisa yarjejeniyar an bayyana cewa ranar 31 ga watan Yuli, ita ce rana ta karshe a matakain farko na yarjejeniyar, koda yake kungiyar ba ta iya gudanar da ayyukan dake kunshe cikin yarjejeniyar yadda ya kamata ba, bisa wannan lokacin da aka tsara.
Game da wannan batu babban sakataren kungiyar ta WTO Roberto Azevedo, ya bayyana cewa bayan zartas da yarjejeniyar samar da saukin gudanar da ciniki a wannan karo, mambobin kungiyar za su fara gudanar da bincike kan yarjejeniyar bisa tsarinsu. (Maryam)