Hukumar cinikayya ta duniya WTO ta gabatar da adadin hasashen da ke nuna karuwar cinikayyar duniya a ranar talata 23 ga wata, inda ta yi hasashe cewa, za a samun karuwa a fannin cinikayyar kasa da kasa da kashi 3.1 bisa dari a shekarar 2014, wanda ya yi kasa da adadin da aka yi a watan Afrilu da ya gabata na kashi 4.7 cikin dari.
WTO ta nuna cewa, ba a samun karuwar tattalin arziki duniya mai kyau a farkon rabin wannan shekara ba, wanda ya yi kasa da hasashen da aka yi a baya, kuma ba a samun bukatun shigo da kayayyaki mai karfi, abin da ya sa aka daidaita hasashe kan karuwar cinikayyar kasa da kasa. (Amina)