in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yaba nadin Yi a matsayin mataimakin darekta a hukumar cinikayya ta duniya
2013-08-18 20:30:21 cri
A ranar lahadin nan ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta yaba nadin wakilin din din din na kasar a hukumar cinikayya ta duniya (WTO), Yi Xiaozhun, a matsayin mataimakin darekta janar na hukumar.

Yi shine basine na farko da ya hau wannan matsayi.

Mai Magana da yawun ma'aikatar Yao Jian ya bayyana cewa nada Mr Yi a kan wannan matsayi ya nuna kwarewarsa da kuma muhimmiyar rawa da kasar Sin da ma sauran kasashe masu tasowa ke takawa a hukumar.

Har ila yau, Yao ya yaba nadin mataimakan darekta janar guda uku da sabon darekta janar din hukumar ya yi .

Banda Mr Yi, sauran wandanda darekta janar din na gaba Roberto Azevedo ya nada su ne, Karl-Ernst Brauner na kasar Jamus, Yonov Frederick Agah na kasar Najeriya da kuma David Shark na kasar Amurka.

Sabon darekta janar din zai kama aikin wa'adinsa daga 1 ga watan satumba kana mataimakan nasa za su fara aiki ranar 1 ga watan Oktoba.(Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China