Cikin jawabinsa na kama aiki a taron musamman na majalisar kungiyar, Azevedo, ya kara da cewa "tsarin cinikayya na bangarorin duniya daban daban hanya ce mafi dacewa ta dakile ra'ayin kariyar cinikayya, shi ne kuma muhimmin mataki da zai taimaka wajen farfado da tattalin arzki da kuma bunkasuwarsa."
Haka zalika, Azevedo ya ce, idan ba a inganta shawarwari ba, hakan zai iya kawo cikas ga sauran ayyukan kungiyar. Ya kara da cewa, "akwai bukatar tabbatar da managartan shawarwari, domin nunawa duniya ikon kungiyar WTO, na iya daddale yarjejeniyar cinikayya tsakanin bangarori da dama. Ya ce akwai bukatar samun nasara a yayin taron ministocin cinikayya da za a shirya a Bali na kasar Indonesiya, aikin da ya ce shi ne na farko da za su sanya a gaba."
Azevedo wanda tsohon jami'in diplomasiyya ne daga kasar Brazil, ya kasance sabon babban daraktan kungiyar ta WTO ne a ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata, zai kuma jagoranci kungiyar zuwa shekaru 4 masu zuwa. (Bilkisu)