Za a fara bukukuwan daga ranar 7 ga wata, a wannan rana, dubun dubantar mutane za su harama a dakin tunawa da kisan kiyashi da aka kebe a Kigali, babban birnin kasar domin tunawa da wadanda suka mutu da yawansu ya kai dubu 250. Haka kuma, za a kunna wutar Kwibuka Flame dake alamta gudanar da bukukuwan a wurare 30 na kasar, har zuwa ranar 7 ga watan Afrilu wato ranar da gwamnatin kasar ta kebe domin tunawa da wannan.
Za a kai wutar da kunna don tunawa da kisan kiyashi a farko zuwa wani dakin tunawa da kisan kiyashi da ke yankin kudancin kasar Rwanda, domin tunawa da daliban da aka kashe a wurin.
Ministan wasannin motsa jiki da al'adu na kasar Protais Mitali ya fada wa manema labaru cewa, dalilin da ya sa aka shirya wadannan bukukuwa shi ne na shaida anniyar jama'ar Rwanda domin magance sake abkuwar irin masifa. Gwamnatin Rwanda ta bukaci jami'an kasar na matakai daban daban da su tashi tsaye domin halarta bukukuwan da za'a shirya, tare da bukatar jama'a shiga taron kara-wa-juna-sani game da tarihin kasar, kuma yana fatan wadannan bukukuwa za su kara hada kan al'ummomin kasar baki daya.
Bisa labarin da aka samu, an ce, ofishin jakadancin kasar Rwanda da ke kasashen waje da jama'ar Rwanda dake kasashen duniya, su ma za su shirya bukukuwa, domin tunawa da zagayowar shekaru 20 da kisan kiyashi a shekarar 1994, inda aka hallaka 'yan kabilar Tutsi da Hutus da yawansu ya kai dubu 800. (Bako)