1110-APEC-fatima
|
Taron na yini biyu dai ya samu halartar shugabannin kasashe membobin kungiyar ta APEC, da shugabannin sassan masana'antu dake yankin Asiya da tekun Pasifik, da shahararrun masana kimanin 1500.
Yayin zaman na jiya an yi musayar ra'ayoyi tare da shawarwari game da karfafa dangantakar abokantaka tsakanin sassan a nan gaba, a kokarin kara bunkasa tattalin arzikin yankin.
Wasu shugabannin kasashe da yankuna da ba sa cikin kungiyar ta APEC, su ma sun bayyana fatansu na shiga kungiyar, domin ba da gudummawarsu a fannin raya tattalin arzikin yankin.
Ko yaya za a iya sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasashe da yankuna na Asiya bai daya? Tun dai bayan da aka cimma matsaya kan taswirar Beijing game da yankin cinikayya mai 'yanci na yankin Asiya da tekun Pasifik a gun taron APEC na wannan rana, an fi mai da hankali kan shawarta yadda za a bi wannan taswira ta hanya mafi dacewa.
Shugabar kasar Chile, madam Michelle Bachelet tana ganin cewa, kamata ya yi wannan yanki ya sami bunkasuwa mai dorewa. Ta ce,
"Muna nuna goyon baya sosai ga gudanar da taswirar kafa yankin cinikayya mai 'yanci a yankin Asiya da tekun Pasifik. Mun yi imanin cewa, za a gudanar da wannan aiki bisa yunkurin da aka samu, ko da ake yin shawarwari a kai wajen samun bunkasuwa tare, kamarsu dangantakar abokantaka ta yankin tekun Pasifik, da yarjejeniyar karfafa huldodin tattalin arziki ta Trans-Pacific wato TPP, da kuma yarjejeniyar kafa dangantakar abokantaka ta fuskar tattalin arziki daga dukkan fannoni a shiyya-shiyya wato RECP. Akwai dangantaka tsakanin wadannan yarjeniyoyi, kuma suna taimakawa juna."
Shugaban kamfanin Caterpillar, Doug Oberhelman ya bayyana cewa, kawo yanzu kamfaninsa ya ninka sau uku bisa yadda yake a shekarar 1989, wanda hakan ya biyo bayan cin gajiyar yunkurin samun bunkasuwa tare, kamar yadda kungiyar APEC take kokarin yi. Mista Oberhelman yana ganin cewa, yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne ra'ayin shugabannin kasashe da yankuna daban daban, na nuna goyon baya da sa kaimi ga cimma yarjejeniyar cinikayya tsakanin bangarori da dama. Ya ce,
"A ganina, abu mafi muhimmanci shi ne shugabannin mambobin kungiyar APEC 21 su nuna goyon baya ga cinikayya da tsarin cinikayya tsakanin bangarori da dama. Ina sanya ran ganin sakamakon yin shawarwari nan da nan. Idan muka iya cimma matsaya cikin sauri, a yanayin da ake ciki a bana na rashin samun karfin bunkasuwa, za mu ga yadda ma'aunin GDP zai karu bisa yadda yake a baya."
Idan ba a manta ba a jiya Lahadi 9 ga wata nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da kebe kudi har dala biliyan 40, domin kafa asusun hanyar siliki. Game da wannan batu, shugaban bankin Sin, Tian Guoli ya bayyana cewa,
"Shugaba Xi ya yi kira da kafa bankin manyan kayayyakin amfanin jama'a na Asiya. Kuma Sin ta kafa wannan asusu tukuna, domin hakan ya bada damar sa kaimi ga sauran kasashe. Ana fatan mafi yawan kasashe da kamfanonin Asiya za su shiga cikin kasuwannin yankin Asiya da tekun Pasifik da kuzarin da ya dace. Gwamnati ta ba da jagoranci, ana fatan kuma kamfanoni za su hada gwiwa da juna. Bankin Sin kuma ba zai rasa wannan dama ba."
Yayin da yake magana da wakilinmu, shugaban tarayyar kungiyar masana'antu ta Thailand, Supant Mongkolsuthree ya bayyana cewa, kamfanoni matsakaita da kanana, da manoma na Thailand za su ci gajiyar kara saurin bunkasa manyan kayayyakin amfanin jama'a, da kara yin mu'amala tsakanin kasashe da yankuna na Asiya da tekun Pasifik. Ya ce,
"Dole ne mu kafa hanyar jirgin kasa mai sauri sosai. Yanzu gwamnatin kasar mu tana shawarwari da Sin da kuma Japan. Hanyar jirgin kasa za ta ba da gudummawa sosai, wadda za ta iya hada yankin arewa da na kudu. Sufuri na da muhimmanci sosai a gare mu, musamman ma a sha'anin noma."
Bayan haka, a wannan karo an gayyaci wasu shugabannin kasashe da ba sa ckin kungiyar APEC halartar wannan taro. Ciki hadda kasashen kamarsu Bangladesh, da Kampuchea, da Laos, da Burma da sauransu.
A kuma jawabansu, sun bayyana fatansu na shiga yunkurin samun bunkasuwa tare a yankin Asiya da tekun Pasifik.
A Litinin din nan ne kuma ake fatan ci gaba da wannan muhimmin taron koli, inda shugaban Rasha Vladimir Putin, da shugaban Amurka Barack Obama da sauransu za su gabatar da jawabansu.(Fatima)