in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin yana da cikakken imani game da makomar yankin Asiya da tekun Fasific
2013-10-08 17:06:59 cri

A ranar 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na kungiyar raya hadin gwiwar tattalin arziki na yankin Asiya da tekun Fasific wato APEC a fannin masana'antu da kasuwanci da aka yi a tsibirin Bali a kasar Indonesiya, inda Shugaban Xi ya yi muhimmin jawabi mai taken "Zurfafa aikin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, don kawo makoma mai haske ga yankin Asiya da tekun Fasific.".

Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga bin alkiblar aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, kuma yana da cikakken imani game da raya tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

A jawabin sa gun bikin rufe taron koli na kungiyar APEC ta fuskar masana'antu da kasuwanci, shugaban Xi, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, aikin farfado da tattalin arzikin duniya na fuskantar rashin tabbas,don haka tattalin arziki na kasashen Asiya da tekun Fasific yana fuskantar kalubale, abinda yasa gamayyar tattalin arziki ta kasashe masu wadata, da gamayyar tattalin arziki ta kasashe masu tasowa, dukkansu suke kokari wajen raya tattalin arziki.Shugaba Xi yace,"Ina ne za a samu sabon kuzari wajen raya tattalin arziki? A ra'ayina shi ne, ya kamata a same ta ta hanyar yin kwaskwarima, da aikin kyautata tattalin arziki, ko kirkiro da sabbin tunani. Ya kamata gamayyar tattalin arziki ta kungiyar APEC ta kara kwarin gwiwa, don sa tattalin arziki na kungiyar APEC da ta taka muhimmiyar rawa wajen aikin farfado da tattalin arziki na duniya."

Daga taron koli na kungiyar G20 da aka yi a birnin St-Petersburg na kasar Rasha zuwa taron koli na kungiyar APEC da aka yi a tsibirin Bali, a koda yaushe shugaba Xi Jinping ya nuna cikakken imanin sa game da tattalin arzikin kasar Sin, sabo da karuwar tattalin arzikin Sin da yawansa ya kai kashi 7.6 cikin 100, kyautatuwar ingancin raya tattalin arzikin kasar, da aikin raya sabbin garurruwa, da horar da kwararru da 'yan kwadago. Shugaban Xi ya bayyana cewa,"Yanzu, batun raya tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wani sabon mataki, kuma ana aikin canja salon raya tattalin arziki da daidaita tsarin raya tattalin arziki. Sabo da haka, ya kamata, a haye wahalhalun da ke gabanmu. Kasar Sin tana son samun ci gaba, sabo da haka, ya kamata a bude kofa da zurfafa aikin yin kwaskwarima daga dukkan fannoni.'

A gaban sauran mambobin kasashen kungiyar APEC, shugaban kasar Sin ya nuna alkiblar zurfafa aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje sannan kuma, bunkasuwar da kasar Sin ta samu, za ta kawo babbar dama ga kasashen da ke yankin Asiya da tekun Fasific.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na dukufa ka'in da na'in wajen kafa tsarin yin hadin gwiwa da ke ketare gabobi biyu na tekun Fasific, wanda zai more wa bangarorin daban daban. Yana mai cewa, "Dalilin da ya sa, tekun Fasific ke da fadi, sabo da babu shingaye a tsakaninsu, sakamakon haka, mu ma, bai kamata mu kawo cikas ga wannan yanki ba. Ya kamata mu yi amfani da wannan dandali na kungiyar APEC, don inganta manufar raya tattalin arziki daga manyan fannoni da sa kaimi ga yin cinikayya cikin 'yanci na wannan yanki, da zurfafa yunkurin dunkulewar wannan yanki bai daya, don kara yalwata dankon zumunci da ke tsakanin gabobi biyu na tekun Fasific, don cimma burin raya yankin Asiya da tekun Fasific cikin dogon lokaci."

Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da abokanta, don shugabanci kasashen duniya da kawo moriya ga bangarorin daban daban, da kuma kawo alheri ga al'ummar mu

A shekarara 2014, kasar Sin za ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar APEC. Daga tsibirin Bali zuwa birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta yi amfani da wannan dama, don karfafa hakikanin hadin gwiwa, don nuna alkiblar raya yankin Asiya da tekun Fasific cikin dogon lokaci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China