in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin cimma burin yarjejeniyar cinikayya cikin yanci tsakanin kasashe da yankunan da ke Asiya da tekun Pacific
2014-11-04 16:28:06 cri

Bana shekaru 13 ke nan tun bayan da kasar Sin ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki na kasashen Asiya da tekun Pacific APEC, taron da ya gudana a birnin Shanghai. A bana ma za ta sake zama mai masaukin bakin taron da zai gudana a nan birnin Beijing.

Tun dai bayan kafuwar APEC, kungiyar ke samun ci gaba a fannin sa kaimi ga yin sauki wajen cinikayya da zuba jari cikin 'yanci, da kuma hadin gwiwa ta fuskar fasahohin tattalin arziki. Amma sakamakon gibin da ke tsakanin mambobin kungiyar a fannin tattalin arziki, da kuma bambancin burin da suke dora muhimmanci a kai a fannin yin cinikayya marasa shinge, don haka ana bukatar ci gaba da kokari a wannan fanni bisa tsarin kungiyar ta APEC.

Idan muka ambaci batun yin cinikayya cikin 'yanci a tsakanin kasashen Asiya da tekun Pacific, lallai ba za a iya mantawa da burin Bogar, wanda aka gabatar a yayin taron shugabannin kungiyar APEC kan tattalin arziki, da aka gudanar a birnin Bogar na kasar Indonesia a shekara ta 1994 ba.

Wannan buri dai ya tabbatar da hanyar da kungiyar za ta bi wajen hadin gwiwa, wato mambobin kungiyar masu ci gaba su cimma burin yin cinikayya cikin 'yanci a shekara ta 2010, yayin da mambobin masu tasowa su cimma wannan buri a shekara ta 2020. Sai dai tambaya a nan ita ce, ta yaya za a cimma cinikayya cikin 'yanci? Wani muhimmin abu shi ne yadda aka soke harajin kwastam da kuma yin cinikayya cikin sauki. Kafin bude taron APEC na bana, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi, ya gabatar da jerin sabbin alkaluma a wannan fanni. Ya ce,

"A cikin shekaru 20 da suka wuce, tun bayan bayar da Sanarwar Bogar, matsakaicin yawan harajin kwastam da aka biya a yankunan Asiya da tekun Pacific ya ragu, da kashi 12 cikin kashi dari, jimillar cinikayya kuwa ta ninka sau 7, baya ga hakan an gudanar da ayyukan hadin gwiwa kusan 200 a fannoni 30 a ko wace shekara, duk wadannan sun ba da muhimmin tasiri ga hadin gwiwar tattalin arziki a shiyya-shiyya."

Kasancewar kungiyar APEC wata kungiyar shiyya-shiyya da ta kunshi kasashe, da yankuna masu ci gaba da masu tasowa, wadanda suke da bambanci sosai kan muradun da za su samu a yunkurin neman yin cinikayya da zuba jari maras shinge. Hakan ya sa abu ne mai wahala a cimma daidaito kan batun rage yawan harajin kwastam da za a karba, da kuma batun samar da kariyar ciniki.

Yanzu haka ana kokarin cimma burin Bogar. Kana a buri nata APEC ta kara taka rawa ga yunkurin neman yin cinikayya, da zuba jari maras shinge, kana wasu mambobin kungiyar sun gabatar da wani ra'ayin kafa yankin ciniki cikin 'yanci na Asiya da tekun Pacific a shekara ta 2006. A yayin taron ministocin kudi na kungiyar APEC da aka gudanar a birnin Qingdao na kasar Sin a watan Mayu na bana, wakilan mambobi 21 na kungiyar sun cimma daidaito kan wannan ra'ayi.

Game da batun, Andrew Rob, ministan cinikayya da zuba jari na kasar Australia ya bayyana cewa,

"A yayin wannan taro, mun yin hangen nesa har na tsawon shekaru 10 zuwa 15. Kamar yadda aka daddale yarjeniyoyi na TPP da RCEP, da sauran jarjeniyoyin da ke tsakanin bangarori biyu, mambobi 21 na kungiyar APEC sun sa hannu kan jerin yarjeniyoyi a tsakaninsu. Muna fatan hada su tare a nan gaba, a kokarin cimma wata yarjejeniyar yin cinikayya maras shinge a nan gaba, wadda dukkan kasashen Asiya da tekun Pacific za su amince da ita."

Yarjeniyoyin TPP da RCEP da Mr. Andrew ya ambata su ne "Yarjejeniyar karfafa huldodin tattalin arziki ta Trans-Pacific" da "Yarjejeniyar kafa dangantakar abokantaka ta fuskar tattalin arziki daga dukkan fannoni a shiyya-shiyya", wadannan yarjeniyoyi na taka muhimmiyar rawa a kasashen Asiya da tekun Pacific a yanzu haka.

Wang Yuzhu, shi ne shugaban sashen nazarin kungiyar APEC da gabashin Asiya na cibiyar binciken kimiyar zaman al'ummar kasar Sin, yana ganin cewa, manufar kafuwar yankin ciniki cikin 'yanci ita ne hada yankunan ciniki cikin 'yanci a da dama bisa tsari na bai daya. Ya kara da cewa,

"A zamanin yau, ya kamata a kalli gaba a fannin bunkasar kungiyar APEC bai daya. Idan har za a iya kafa yankin ciniki maras shinge a kasashe, da yankuna mambobin kungiyar APEC, to haka zai ba da babban taimako ga karuwar tattalin arzikin yankin kasashen Asiya da na tekun Pacific a nan gaba. Dalilin da ya sa kasar Sin ta gabatar da wannan shiri ya wuce batun aniyar kiyaye da bunkasa APEC, kari a kan hakan akwai fatan kago wata babbar kasuwa a wannan yanki, domin sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China