Daga ranar 6 zuwa ranar 9 ga wata, shugaban kasar Sin, Hu Jintao, ya halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pasific (APEC) karo na 20 da ya gudana a Vladivostok na kasar Rasha. Bayan taron, ministan harkokin wajen kasar Sin, Yang Jiechi, ya gaya wa manema labaru cewa, shugaba Hu ya bayyana a wajen taron niyyar kasar Sin na raya kanta tare da kokarin tabbatar da samun ci gaba a yankin da take ciki na Asiya da tekun Pasific.
A halin da ake ciki, wasu matsaloli masu tsanani dake addabar tattalin arzikin duniya na yin tasiri kan yankin Asiya da tekun Pasific, wadanda suka haifar da wani yanayi mai sarkakiya ga ci gaban tattalin arzikin yankin, da hadin kan kasashen yankin. A bisa wannan yanayi ne an kira kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, bisa babban jigon 'gaurayawa domin ci gaba, da kirkiro sabbin fasahohi domin samun walwala', tare da mai da hankali kan batutuwan da suka hada da cinikayya da zuba jari cikin 'yanci, dunkulewar tattalin arzikin yankin, kokarin samar da isashen hatsi, da dai makamantansu. A wajen taron, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi jawabi, inda ya bayyana matsayin kasar Sin, kana ya yi musayar ra'ayi tare da shugabanni da kwararrun da suka halarci taron.
Kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin, Yang Jiechi, ya fada, bangaren kasar Sin ya taka muhummiyar rawa a kokarin tabbatar da samun sakamako a wannan taron. A cikin jawabinsa, shugaba Hu, da farko ya bayyana matsayin kasar Sin na kokarin ciyar da tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasific gaba, kana ya nanata cewa, kokarin tabbatar da samu karuwa, da zaman karko, da yunkurin neman ci gaba sun kasance manyan ayyuka dake gaban kasashen Asiya da tekun Pasific, musamman ma ta la'akari da yanayin da ake ciki, don haka ya kamata bangarori daban daban su kara azama kan gyare-gyare da hadin kansu don tabbatar da ci gabansu, da sa kaimi ga yunkurin daidaita tsarin da ake bi wajen kula da tattalin arzikin duniya, da gaggauta gyara dabarar raya tattain arziki, da kokarin aiwatar da shawarwarin zagayen Doha, tare da kafa wata huldar abokantaka ta daidaito a tsakanin kasashe dake neman ci gaba.
Har ila yau, minista Yang Jiechi na ganin cewa, jawabin shugaban Hu ya sheda yadda kasar Sin ke neman kara yin hadin kai a tsakaninta da membobin kungiyar APEC. Ya ce, shawarwarin da kasar Sin ta gabatar sun hada da kokarin yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci, da neman kafa wasu yankunan ciniki cikin 'yanci a kasashen Asiya da tekun Pasific. Sa'an nan kan batun samar da isashen hatsi, kasar Sin tana son inganta ayyukan gona, da kara gina kayayyakin more rayuwa a kasuwanni masu sayar da hatsi, da hana hauhawar farashin hatsi, da dai sauransu. Kana game da batun kirkiro sabbin fasahohi na kimiyya da fasaha, kasar Sin ta bukaci a kara zuba kudi kan bincike, da kara kokarin horar da kwararru, da hadin kai kan yaduwa da musayar fasahohi.
Ban da haka, ana ganin cewa, yadda za a sayar da kayayyakin da suka shafi muhalli cikin 'yanci yana da babbar ma'ana ga yunkurin tabbatar da samun karuwar tattalin arziki tare da kiyaye muhalli, wanda zai kara azama ga kokarin yin ciniki cikin 'yanci. Don haka, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya jaddada cewa, kamata ya yi, a yi la'akari da matsayin da kasashe daban daban suka cimma wajen samun ci gaba, da taimakawa kasashen dake tasowa wajen raya harkar da ta shafi muhalli, da tabbatar da samun ci gaba mai dorewa. A wajen taron, kasar Sin ta yi mu'amala sosai tare da sauran bangarori, inda ta ba da gudummawa wajen tsara wani jerin sunayen kayayyaki masu alaka da muhalli wanda ya kunshi kayayyaki 54.
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Yang Jiechi, ya kara da cewa, furucin shugaba Hu na kasar Sin ya yi jagora kan yadda za a raya kungiyar APEC a nan gaba. Ya ce, kungiyar ta riga ta zama wani bangaren dake taka muhimmiyar rawa kan aikin kyautata tsarin kula da tattalin arzikin duniya, da karfafa hadin gwiwar da ake yi a yankin Asiya da Pasific, wadda ita ma tana fuskantar wani sabon yanayi. A wajen taron, shugaba Hu Jintao ya yi kira ga membobin kungiyar da su tsaya kan zama tsintsiya madaurinki daya, da nuna sassaucin ra'ayi kan kokarin tattaunawa don samun matsaya daya, da girmama bambancin da ake da shi, da kokarin sanya hadin kai ya amfana wa juna, da bude kofa da yin hakuri da juna, don nema raya hadin gwiwa a wannan yankin zuwa wani sabon matsayi. Ban da haka, Hu ya ce, kasar Sin na son karbar bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC na shekarar 2014. Hakan zai zama karo na 2 da kasar Sin ta shirya taron bayan shekaru 13 da suka wuce, abin da ya nuna niyyar kasar ta karfafa hadin kai a wannan yankin.
A karshe minista Yang Jie Chi ya ce, kasar Sin ba za ta samu ci gaba ba, in ba tare da hadin gwiwa da sauran kasashen da ke yankin Asiya da tekun Pasific, kana yankin shi ma ba zai yiwu ba ya samu walwala, idan bai sanya kasar Sin cikin tsarinsa ba. Don haka, kasar Sin za ta ci gaba da kokari tare da sauran bangarori, don tabbatar da makomar yankin mai haske, inda za a samu zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tabbatar da walwalar bai daya. (Bello Wang)