in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kara zama mai fada a ji a duniya a fannin tattalin arziki
2014-11-03 17:02:45 cri

Za a gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Asiya da na tekun Pasifik, a fannin tattalin arziki na APEC karo na 22 a nan birnin Beijing, daga ranar 10 zuwa ta 11 ga watan nan da muke ciki. Wannan ne dai karo na biyu da kasar Sin za ta karbi bakuncin taron, bayan da aka yi taron shugabannin APEC a Shanghai a shekarar 2001. Idan an waiwayi wadannan shekaru 13 da suka wuce, za a ga kasar Sin ta kara zama mai fada a ji a duniya musamman ma a fannin tattalin arziki.

An gudanar da taron kolin kungiyar APEC a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin shekaru 13 da suka wuce. Ya zuwa yanzu wannan birni ya kara samun wani yanayi na zama cibiyar duniya ta fuskar hada-hadar kudi.

Bayan da aka kebe wani yankin ciniki mai 'yanci a birnin a watan Satumban bara, an kara tabbatar da sanya bankin raya kasashen kungiyar BRICS a can. Yanzu haka a kan ji sunan birnin yayin da ake sauraron labaru musamman ma wadanda suka shafi tattalin arziki.

Zuwa ranar 18 ga watan Satumban bana, cibiyar musayar zinariya ta birnin Shanghai, ta kafa wani reshen ciniki cikin yankin ciniki mai 'yanci na birnin, inda masu zuba jari na kasashen waje za su iya saye da sayarwa da zinariya kai tsaye. Ta wannan mataki, ana da niyyar kafa wata kasuwar musayar zinariya da za ta yi tasiri a duniya. Game da hakan, mista Zhou Xiaochuan, gwamnan babban bankin kasar Sin, ya bayyana cewa,

"Bisa yanayin ikon ciniki mai 'yanci na Shanghai, da yanayin lokacin da nahiyar Asiya take ciki, gami da farashin da za a nuna ta kudin Sin RMB, wannan cibiyar musayar zinariya za ta kara janyo zinariya cikin kasuwannin kasar Sin, da taka rawar gani a fannin tabbatar da farashin zinariya."

Hakika yadda birnin Shanghai ke kara taka muhimmiyar ruwa a fannin tattalin arziki, ya nuna yadda kasar Sin take kara zama mai fada a ji a duniya a wannan bangare. A shekarar 2001, kasar Sin ta kasance kan matsayi na 6 a duniya bisa yawan kudin tattalin arzikinta na dala biliyan 1150, amma zuwa yanzu ta riga ta hau matsayi na 2 a duniya. Musamman ma bayan da aka samu tabarbarewar tattalin arzikin duniya a shekarar 2008, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya kara zama wani karfin dake tura tattalin arzkin duniya gaba.

Dangane da haka, madam Christine Lagarde, shugabar asusun ba da lamuni na IMF, ta ce,

"Yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta sake shaida karfinta a fannin ba da jagoranci, bisa samun ci gaba sosai a fannin tattalin arziki. Yanzu kasar Sin a matsayinta na daya daga cikin masu hannun jari mafi girma a asusun IMF, kuma wadda ke da tasiri sosai cikin kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, tana taka muhimmiyar rawa a fannin kare ingancin tattalin arzikin duniya."

Sakamakon hauhawar matsayin kasar Sin a fannin tattalin arzikin duniya, asusun ba da lamuni na IMF ya kara ba ta kuri'u, wadda za ta yi amfani da ita yayin da ake neman yanke wata shawara cikin asusun, ta yadda kasar ta daga matsayinta zuwa ta 3 wajen yawan mallakar kuri'un. Haka zalika, kasar ta kara zama mai fada a ji a fannonin masana'antu, kudi, da cinikin duniya. A cewar Shen Jiru, shahararren masanin tattalin arzikin kasar Sin, hauhawar matsayin kasar Sin a tattalin arzikin duniya ita ce ta sa kasar ta kara zama mai fada a ji.

"Cikin karfin da yake tura tattalin arzikin duniya gaba, kasar Sin ta samar da daya daga cikin ukunsa. Kana a fannin cinikayya, kasar ta zama mafi karfi a duniya bisa yawan kudin ciniki na dalar Amurka biliyan 4000. Saboda haka wannan karuwar tattalin arziki ta sanya kasar ta zama mai fada a ji a duniya. Domin idan wata kasa tana da karfin tattalin arziki sosai, kuma cinikin da ake yi tsakaninta da sauran kasashe ya yi yawa, to, za a saurari ra'ayinta kafin a tabbatar da wasu tsare-tsare a bangaren tattalin arziki."

Dangane da taron APEC da zai gudana a birnin Beijing a watan da muke ciki, wasu masana sun lura da wasu sabbin abubuwa da aka ambata game da babban jigon taron, wanda zai sa taron kasancewa mai amfani idan an kwatanta da taron da aka gudanar a birnin Shanghai shekaru 13 da suka wuce. A taron da aka yi a Shanghai an bayyana bukatar yin ciniki cikin 'yanci, sa'an nan a wannan karo ma za a tattauna kan wasu muhimman matakan da za a iya dauka a wannan fanni.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China