A ranar 20 ga wata, bangarori biyu na dakarun jama'a sun sake rikici da juna don tafutukar kwace filin jiragen sama na duniya a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya, wannan dai ya nuna cewa, yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka daddale a da ta ci tura.
Rashin kafa wani tsarin sojoji a hukunce bayan yakin Libya, a halin yanzu bangarori biyu da ke rikici da juna a tsakanin dakarun jama'a a Misrata da Zintan sun kasance dakarun da suka fi karfi a kasar, sakamakon haka ne ma, wasu kasashen waje ke nuna damuwar cewa, mai yiyuwa ne ba za a iya daukar wani mataki a halin da ake ciki a Libya. (Danladi)