A wannan rana, kwamitin sulhu ya gudanar da taro a bainar jama'a kan batun Libya, inda Liu Jieyi ya bayyana cewa, ana gudanar da shirin mika mulkin kasar Libya cikin hali mai kyau bisa kokarin gwamnatin kasar.
Mr. Liu ya kara da cewa, kasar Sin ta goyi bayan ci gaba da gudanar da shirin mika mulki a kasar Libya, kuma tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa su mai da hankali kan moriyar jama'ar kasa da kuma kiyaye dinkuwar kasa, warware sabanin da ke tsakanin bangarori daban daban ta hanyar yin shawarwari, fuskantar kalubalolin da suka gamu da su yayin gudanar da shirin mika mulki yadda ya kamata don cimma burin samun jituwar kabilun kasar da sauri da kuma gaggauta ayyukan farfadowa da kuma neman ci gaban kasa. (Maryam)