An bude babban taron Afrika karo na 10 kan ilimin halittu tun ranar Litinin a birnin Brazzaville na kasar Congo, tare da halartar ministan harkokin jama'a, jin kai da taimakon juna na kasar Congo, wanda ya jaddada wajabcin samun kayayyakin aikin a fannin likitanci da bukatar kwararru a fannin ilimin halittu. Bisa taken "fasahar ilimin halittu, kiwon lafiyar jama'a, da gwaje-gwajen yaki da cuta", kuma wadannan shawarwari za su kwashe kwanaki biyar wanda a cewar minista Emilienne Raoul, lokaci ne mai muhimmanci wajen ganin gwaje-gwaje ko bincike su kasance ayyuka masu karfi da inganci wajen taimakawa samun sauki ga masu fama da rashin lafiya. (Maman Ada)