in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar dumokradiyar Congo ta mika dakaru ga rundunar yanki ta AU don fafatawa da kungiyar 'yan tawaye ta LRA
2013-02-16 16:18:22 cri

Kungiyar AU ta ba da sanarwa ranar Juma'a cewa, jamahuriyar dumokradiyar Congo ta mika sojoji guda 500 ga rundunar kungiyar hada kan kasashen Afirka ta yanki wato RTF don murkushe dakarun 'yan tawayen kungiyar Lord's Resistance Army (LRA).

A ranar Laraba ne aka yi bukin mika sojojin a garin Dungu, hedkwatar dakarun yakin ta RTF dake arewa maso gabashin kasar jamhuriyar dumokradiyyar Congo, in ji kungiyar ta AU.

Manjo janar Amuli Bahigwa wanda shi ne babban hafsa mai kula da harkokin sojojin kasar (FARDC) shi ne ya mika dakarun ga Francisco Madeira, wanda shi ne wakili na musamman na shugabar hukumar gudanar da harkokin kungiyar AU kan batun 'yan tawayen na LRA.

Daga cikin wadanda suka halarci bukin mika dakarun, akwai wakilin musamman na babban magatakardan MDD kuma shugaban ofishin MDD a yankin tsakiyar Afirka Abou Moussa, da ma wasu manyan mutane da kuma manyan jami'an soja.

Mika wadannan sojoji da za su yaki 'yan tawayen kungiyar LRA ya dace ne da matakai da aka cimma yayin wata ganawar hadin gwiwa don kawar da 'yan tawayen LRA wanda aka yi a ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2012 a birnin Addis Ababa.

A cikin watan Satumba na shekarar 2012, gwamnatin jamhuriyar tsakiyar Afirka (CAR) ta ba da gudummawar sojoji guda 350, sannan kasashen Sudan ta kudu da Uganda sun mika sojoji sama da 500 da 2000 daki daki ga rundunar ta RTF.

Bayan mika dakaru guda 500 da jamhuriyar demokradiyar Congo ta yi, yanzu yawan sojojin sun kai 3350 wadanda su ne za'a dukufa kan yaki da 'yan tawayen LRA a shiyyar Dungu, wato ke nan banda wadanda ake da su a shiyoyin Nzara dake Sudan ta kudu da kuma na Obo a jamhuriyar dumokradiyar Congo, in ji sanarwa da kungiyar AU ta bayar.

Kungiyar ta AU ta yi kiran samar da kyakyawan gudanarwa da kuma karin gudummawa daga abokan hadin gwiwa a kokarinta na ganin an murkushe 'yan tawayen kungiyar LRA don tabbacin samun daidaito a yankin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China